Kamfanin Turkish Airlines zai kara yawan jiragen da ke zuwa Uzbekistan

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama da ke da alaka da Ma’aikatar Sufuri ta Uzbekistan ta ba wa kamfanin jiragen saman Turkiyya na Turkish Arlines izinin zirga-zirgar jiragen sama daga Istanbul zuwa biranen Urgenc da Fergana.

1625171

A cikin sanarwar da Ma’aikatar ta fitar, an tunatar da cewa a halin yanzu kamfanin na Turkish Airlines na shirin zirga-zirgar jiragen sama zuwa Tashkent da Samarkand.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu wanda ya gudanar da taro a Uzbekistan a watan jiya ya bayyana cewa sun tattauna batun karin jiragen da ke tsakanin kasashen biyu tare da Uzbekistan.Labarai masu alaka