An kubutar da 'yan gudun hijira 18 a tekun Turkiyya

A gabar tekun Gelibolu da ke Turkiyya an kubutar da 'yan gudun hijira 18 bayan da jami'an tsaron tekun Girka suka yi watsi da su a tekun.

1625252
An kubutar da 'yan gudun hijira 18 a tekun Turkiyya

A gabar tekun Gelibolu da ke Turkiyya an kubutar da 'yan gudun hijira 18 bayan da jami'an tsaron tekun Girka suka yi watsi da su a tekun.

Jami'an tsaron tekun Turkiyya sun samu labarin ganin 'Yan gudun hijira a cikin jirgin ruwan roba a gabar tekun gundumar Ayvacik inda nan da nan suka bazama.

Jami'an tsaron sun kubutar da 'yan gudun hijirar su 18 wadanda jami'an tsaron tekun Girka suka kora zuwa iyakar teku ta Turkiyya.

Bayan kammala tantance 'yan gudun hijirar, an mika su ga helkwatar Mayar da 'Yan Gudun Hijira Kasashensu da ke Ayvacik.

 Labarai masu alaka