Turkiyya ta yi tir da Allah wadai akan harin da lsra'ila ta kai Gaza

Mai magana da yawun shugaban kasar Turkiyya Ibrahim Kalin ya yi tir da Allah wadai akan hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama a yankin Zirrin Gaza

1622761
Turkiyya ta yi tir da Allah wadai akan harin da lsra'ila ta kai Gaza

Mai magana da yawun shugaban kasar Turkiyya Ibrahim Kalin ya yi tir da Allah wadai akan hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama a yankin Zirrin Gaza. 

Kalin ya yada a shafukansa na sadar da zumunta da cewa,

"Muna masu matukar nuna kyama da yin Allah wadai akan hare-haren da Isra'ila ta kai yankin Zirrin Gaza a cikin wannan watan na Ramadan mai alfarma.  Turkiyya na kara bayyana mastayinta na taimakawa da kasancewa tare da Falasdin a yunkurin kalubalantar cin zalim da kasar lsraila ke yi ma ta. Muna masu kira ga lsraila da ta dakatar da irin wadanan hare haren na kin kari."Labarai masu alaka