Ana ci gaba da yaki da Covid-19 a Turkiyya

A awanni 24 da suka gabata mutane 288 sun sake rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.

1623272
Ana ci gaba da yaki da Covid-19 a Turkiyya

A awanni 24 da suka gabata mutane 288 sun sake rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.

Tun daga farkon bullar annobar zuwa yau, jimillar mutane dubu 35,608 ne suka mutu a kasar.

A rana guda an yi wa mutane 319,316 gwaji inda aka samu 62,606 na dauke da cutar, kuma 2,973 na da alamun rashin lafiya.

Karin mutane 52,184 sun warke wanda ya kawo adadin wadanda suka warke daga cutar zuwa miliyan 3 da dubu 643 da 734.

 Labarai masu alaka