Corona ta yi ajalin karin mutane 289 a Turkiyya

A awanni 24 da suka gabata mutane 289 sun sake rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.

1622880
Corona ta yi ajalin karin mutane 289 a Turkiyya

A awanni 24 da suka gabata mutane 289 sun sake rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.

Tun daga farkon bullar annobar zuwa yau, jimillar mutane dubu 35,320 ne suka mutu a kasar.

A rana guda an yi wa mutane 320,078 gwaji inda aka samu 63,082 na dauke da cutar, kuma 2,915 na da alamun rashin lafiya.

Karin mutane 56,510 sun warke wanda ya kawo adadin wadanda suka warke daga cutar zuwa miliyan 3 da dubu 591 da 550.

Labarai masu alaka