An gano makaman da aka kaiwa sansanin sojan Turkiyya hari dasu a Mosul

An bayyana cewa makaman harba rokoki da aka yi amfani da su wajen kai harin roka kan sansanin Turkiyya da ke Bashika, inda wani soja ya yi shahada, suna a wani wuri da ke karkashin ikon Hashd al-Shaabi a Mosul

1622170
An gano makaman da aka kaiwa sansanin sojan Turkiyya hari dasu a Mosul

An bayyana cewa makaman harba rokoki da aka yi amfani da su wajen kai harin roka kan sansanin Turkiyya da ke Bashika, inda wani soja ya yi shahada, suna a wani wuri da ke karkashin ikon Hashd al-Shaabi a Mosul.

Rafet Simo, mataimakin gwamnan Mosul, ya ba da sanarwa ga wani kamfanin buga littattafan Rudaw da ke Erbil. Inda yake cewa,

"An gano makaman harba makami mai linzami da aka kaiwa sansanin sojan Turkiyya hari dasu  a yankin Birged na 30 na Hashd (Hashdi Shabi), tsakanin yankunan Shalalat da Baveza." 

Ma’aikatar Tsaron kasar Turkiyya ta sanar da cewa wani soja ya yi shahada a harin roka da aka kai a cikin sansanin na Basika.

A cikin sanarwar, an ba da rahoton cewa daya daga cikin rokoki uku da aka harba ya fada cikin sansanin  biyu kuma a wani kauye lamarin da ya yi sanadiyar raunanan wani mutum.

 Labarai masu alaka