Corona ta yi ajalin karin mutane 211 a Turkiyya

A awanni 24 da suka gabata mutane 211 sun sake rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.

1616040
Corona ta yi ajalin karin mutane 211 a Turkiyya

A awanni 24 da suka gabata mutane 211 sun sake rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.

Tun daga farkon bullar annobar zuwa yau, jimillar mutane dubu 32,667 ne suka mutu a kasar.

A rana guda an yi wa mutane 271,547 gwaji inda aka samu 49,584 na dauke da cutar, kuma 2,003 na da alamun rashin lafiya.

An kuma sallamar karin mutane 28,498 wanda ya kawo adadin wadanda aka sallama zuwa miliyan 3 da dubu 159 da 475.

 Labarai masu alaka