An kubutar da 'yan gudun hijira 24 a tekun Turkiyya

A gabar tekun gundumar Ayvalik da ke lardin Balikesir na Turkiyya an kubutar da 'yan gudun hijira a lokacin da su ke kokarin tafiya Tsibirin Lesbos na Girka.

1615377

Jami'an Tsaron Tekun Turkiyya ne suka kubutar da 'yan gudun hijirar bayan samun labarin taimakon da su ke nema a mashigar Tsibirin Ciplak sakamakon lalacewar jirgin ruwan robar da su ke ciki.

Jami'an da aka aika wajen sun kubutar da 'yan gudun hijira 'yan kasashen waje su 24.

An kai 'yan gudun hijirar zuwa ga Ofishin Jami'an Tsaron Teku da ke Ayvalik.Labarai masu alaka