An kubutar da 'yan gudun hijira 71 a tekun Turkiyya

Jami'an tsaron teku na Turkiyya sun kubutar da 'yan gudun hijira a gabar tekun gundumomin Dikili da Cesme da ke lardin Izmir bayan da jami'an tsaron tekun Girka suka kora su ruwan Turkiyya.

1610914

Bayan samun labarin ganin 'yan gudun hijira a jirgin ruwa a gabar Cesme ne ya sanya aka aika da jami'an tsaro.

An kubutar da 'yan gudun hijirar da jami'an tsaron Girka suka kora su zuwa ruwan Turkiyya a jirgin ruwan roba.

Haka zalika jami'an tsaron tekun na Turkiyya sun kubutar da 'yan gudun hijira 43 a gabar tekun gundumar Dikili bayan kora su ruwan kasar da sojojin teku na Girka suka yi.

Bayan tantance 'yan gudun hijirar su 71 da suka hada da mata da yara kanana, an aika su zuwa helkwatar Hukumar Kula da Shige da Fice ta Izmir.

A ranar Litinin din nan am an kubutar da 'yan gudun hijira 144 a gabar tekun lardunan Canakkale, Balikesir da Mugla da ke Turkiyya. An gano cewa, jami'an tekun Girka ne suka kora mutanen zuwa iyakar teku ta Turkiyya.Labarai masu alaka