Turkiyya na cigaba da gasawa kunyar ta’addar ISIS aya a hannu

Turkiyya na ci gaba da kara karfin gwiwa wajen yaki da kungiyar ta’addar Deash wacce kuma aka sani da sunan ISIS a farmakan da ta kaddamar a watan Febrairu

1596269
Turkiyya na cigaba da gasawa kunyar ta’addar ISIS aya a hannu

Turkiyya na ci gaba da kara karfin gwiwa wajen yaki da kungiyar ta’addar Deash wacce kuma aka sani da sunan ISIS a farmakan da ta kaddamar a watan Febrairu.

Dakarun kasar sun yi kokarin kauda wasu hare-hare da dama a yankin musanman a yankunan Istanbul da Ankara da kuma a yankin yammacin gundumar Adana.

A farmakan an tsare wadanda ake zargi da ta’addanci har mutum 165 a watan jiya. An kuma daure 55 inda kuma aka yi nasarar kwace makamai da sauran kayayyakin ‘yan ta’addan kamar yadda kanfanin dillacin labaran Anadolu ta sanar.Labarai masu alaka