Mata sun fi maza tsawon rayuwa a Turkiyya

A yayinda kason mata a kasar Turkiyya ya ke 49.9 cikin dari, tsawon rayuwa a kasar ya kasance shekaru 78.6 a tsakaice inda na mata ya kasance shekaru 81.3 na maza kuwa shekaru 75.9 ne

1595964
Mata sun fi maza tsawon rayuwa a Turkiyya

A yayinda kason mata a kasar Turkiyya ya ke 49.9 cikin dari, tsawon rayuwa a kasar ya kasance shekaru 78.6 a tsakaice inda na mata ya kasance shekaru 81.3 na maza kuwa shekaru 75.9 ne.

Hukumr kididigar kasar Turkiyya ta fitar da "kididdigar mata 2020"

Akan hakan an bayyana cewa kaso 49.9 cikin al'umman kasar mata ne inda kaso 50.1 suka kasance maza. Yawan mata a kasar Turkiyya ya kai miliyan 41 da dubu 698 da dari 377 inda yawan maza kuwa ya ke miliyan 41 da dubu 915 da 985.

Bisa ga alkaluman wadanda suka fi dadewa a duniya tsakanin mata da zama, alkaluman sun bayyana cewa mata sun fi maza jimawa a doron kasa.

Yayinda matsakaicin tsawon rayuwar a kasar Turkiyya yake shekara 78.6 matsakaicin tsawon rayuwar mata ya kasance shekaru 81.3 yayinda na maza kuwa ya ke 75.1.

 

 Labarai masu alaka