Jan Kubis zai ziyarci Turkiyya

Wakilin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) na musamman a Libiya kuma Shugaban Ofishin Majalisar Dinkin Duniya na tallafawa Libiya, Jan Kubis zai ziyarci Turkiyya daga ranar 2 zuwa 3 ga Maris din 2021.

1593079

A cikin sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar game da batun, an bayyana cewa,

"Wakilin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Libiya kuma Shugaban Ofishin Majalisar Dinkin Duniya na tallafawa Libiya, Jan Kubis zai ziyarci kasarmu a daga ranar 2 zuwa 3 ga Maris din 2021."

Ana hasashen cewa Kubis da Ministan Harkokin Waje, Mevlut Cavusoglu wanda zai karbi bakuncinsa za su tattauna kan tsarin siyasa da ke gudana tsakanin 'yan Libiya da kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.Labarai masu alaka