Alluran riga-kafin Corona miliyan 6 daga China sun isa Turkiyya

Kashi na 2 na alluran riga-kafi da Turkiyya ta saya daga China sun sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Istanbul.

1570835
Alluran riga-kafin Corona miliyan 6 daga China sun isa Turkiyya

Kashi na 2 na alluran riga-kafi da Turkiyya ta saya daga China sun sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Istanbul.

Jirgin saman Turkish Airlines samfurin Boeing 777 mai lamba TK 6175 ya sauka a filin tashi da saukar jiragen saman Istanbul da misalin karfe 6.00 na safiyar Litinin din nan.

Jirgin ya taso daga filin tashi da saukar jiragen sama na Beijing Babban Birnin China, kuma bayan ya sauka a Istanbul an tantance kayan tare da kai su ma'ajiyarsu.

An bayyana cewar jirgin ya kawo allurai miliyan 6,5, kashin farko na allurai miliyan 10 da Turkiyya ta sake saya daga wajen China.Labarai masu alaka