Adadin masu kamuwa da Corona a Turkiyya na raguwa sosai
A awanni 24 da suka gabata mutane 140 sun sake rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.
1570047

A awanni 24 da suka gabata mutane 140 sun sake rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.
Tun daga farkon bullar annobar zuwa yau, jimillar mutane dubu 25,073 ne suka mutu a kasar.
A rana guda an yi wa mutane 148,425 gwaji inda aka samu 5,277 na dauke da cutar, kuma 684 suna kwance a asibiti.
An kuma sallami karin mutane 5,860 wanda ya kawo adadin wadanda aka sallama zuwa miliyan 2 da dubu 307 da 721.