An kassara 'yan ta'addar PKK 4 a arewacin Iraki

Turkiyya na yaki da 'yan ta'addar a ware na PKK a ciki da wajen ta.

1569287
An kassara 'yan ta'addar PKK 4 a arewacin Iraki

A wasu farmakai ta sama da aka kai a yankin Gara na arewacin Iraki, an kassara 'yan ta'addar a ware na PKK 4.

Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta sanar da cewa,

"Sakamakon aiyukan da dakarunmu da na hukumar leken asiri suka yi, an kai garmaki ta sama tare da kassara 'yan ta'addar a ware na PKK 4 a yankin Gara na arewacin Iraki."Labarai masu alaka