Corona ta yi ajalin mutane 75 a Turkiyya

A awanni 24 da suka gabata mutane 75 sun sake rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.

1516414
Corona ta yi ajalin mutane 75 a Turkiyya

A awanni 24 da suka gabata mutane 75 sun sake rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.

Tun daga farkon bullar annobar zuwa yau, jimillar mutane dubu 9,874 ne suka mutu a kasar.

A rana guda an yi wa mutane 132,913 gwaji inda aka samu 2,198 na dauke da cutar.

An kuma sallami karin mutane 1,618 wanda ya kawo adadin wadanda aka sallama zuwa dubu 316,008.Labarai masu alaka