Dubun kungiyoyi masu fataucin miyagun kwayoyi ta cika a Turkiyya

Rundunar ‘yan sanadan kasar Turkiyya ta kwace miyagun kwayoyi da ya kai kusan kilogiram 80 da suka kunshi marijuana a wani farmakin yaki da miyagun kwayoyi da suka kaddamar

1493627
Dubun kungiyoyi masu fataucin miyagun kwayoyi ta cika a Turkiyya

Rundunar ‘yan sanadan kasar Turkiyya ta kwace miyagun kwayoyi da ya kai kusan kilogiram 80 da suka kunshi marijuana a wani farmakin yaki da miyagun kwayoyi da suka kaddamar.

A tsakiyar gundumar Aksaray ‘yan sanda sun kwace miyagun kwayoyi har guda dubu 23,000 kusan kilo 79.7 na Marijuana.

An farmakin miyagun kwayoyin an kame wasu mutum biyu wadanda aka gurfanar a gaban kuliya.

Kotun dai ta daure mutum biyun bayan ta kamasu da laifin aikata fataucin miyagun kwayoyi.

Haka kuma a gundumar Hatay jami’an ‘yan sanda sun cika hannu da wasu mutum biyu bayan karnukan dake iya gane da bayyana miyagun kwayoyi sun nuna alamar cewa suna dauke da miyagun kwayoyin da bincike ya nuna cewa sun kwara dubu 1,890 a cikin motarsu.

 

 Labarai masu alaka