"Ba zamu yarda da kalaman raini ga shugaba Erdoğan ba"

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu ya bayyana cewa ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta gayyaci jakadan Girka a Turkiyya akan kalaman raini ga shugaba Erdogan da wata jaridar kasar Girka ta yada a kanun labaranta

1493523
"Ba zamu yarda da kalaman raini ga shugaba Erdoğan ba"

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu ya bayyana cewa ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta gayyaci jakadan Girka a Turkiyya akan kalaman raini ga shugaba Erdogan da wata jaridar kasar Girka ta yada a kanun labaranta.

Minista Mevlüt Çavuşoğlu, ya shaidawa kanfanin dillancin labaran Anadolu da cewa,

"Ma'aikatar diflomasiyarmu ta gayyaci Jakadan Girka a Turkiyya akan kalaman raini da batanci da wata jaridar kasar Girka ta yi ga shugaba Recep Tayyip Erdoğan.

Ya kara da cewa "A kafafen yada labaranmu za'a iya samun masu sukar 'yan siyasar Girka, muma sukan sokemu, sosai ma kuwa. Amma zagi da cin mutunci ya sabawa ka'iadar harkokin watsa labarai. Ma'aikatar sadarwar Turkiyya ma na duba lamarin da idon basira, zamu dauki matakan da suka dace"

 Labarai masu alaka