Erdogan: Turkiyya na kusa da samar da allurar riga-kafin Covid-19

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa akwai yiwuwar Turkiyya ta samar da allurar riga-kafin Covid-19 bayan sabuwar shekara

1493579
Erdogan: Turkiyya na kusa da samar da allurar riga-kafin Covid-19

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa akwai yiwuwar Turkiyya ta samar da allurar riga-kafin Covid-19 bayan sabuwar shekara.

Likitoci da masana kimiyya da fasaha a kasar Turkiyya dai sun kasance suna aiki tukuru domin samar da mafita tun bayan barkewar cutar corona a doron kasa.

Masana harkokin magani a kasar sun samar da maganin Covid-19 mai suna Favipiravir wanda ya samu karbuwa kwarai da gaske a fadin duniya.Labarai masu alaka