Corona: Turkiyya ta aike da kayan taimako zuwa Paraguay

Turkiyya ta aike da kayan taimako don yaki da annobar Corona (Covid-19) a kasar Paraguay.

1432925
Corona: Turkiyya ta aike da kayan taimako zuwa Paraguay

Turkiyya ta aike da kayan taimako don yaki da annobar Corona (Covid-19) a kasar Paraguay.

Rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Paraguay ta fitar ta bayyana cewar Shugaban kasar Mario Abdo Benitez da matarsa Silvana Abdo ne suka nemi taimako daga wajen Shugaban Kasar Turkiyya Recep tayyip Erdogan da mai dakinsa Emine Erdogan don yaki da annobar Corona.

Bayan Emine Erdogan ta amince da a bayar da taimakon ne sai Ma'aikatun Lafiya da na Harkokin Wajen Turkiyya da Paraguay suka fara aiyuka tare. An kuma aika da kayan zuwa Paraguay ta kasat Barazil.

Kayan da ake sa ran za su isa Paraguay nan da wasu 'yan kwanaki sun hada da rigunanan kariya dubu 50, takunkumin rufe baki samfurin N95 dubu 30, takunkumin tiyata na likitoci guda dubu 100 da tabarau dubu 2.Labarai masu alaka