Ana cigaba da samun raguwar masu kamuwa da Corona a Turkiyya

Ministan harkokin kiwon lafiyar kasar Turkiyya Dkt. Fahrettin Koca ya bayyana cewa duk da karin yawan wadanda akeyiwa gwajin Covid-19 a ‘yan kwanakin nan ana ci gaba da samun raguwar masu kamuwa da cutar a rana

1422328
Ana cigaba da samun raguwar masu kamuwa da Corona a Turkiyya

Ministan harkokin kiwon lafiyar kasar Turkiyya Dkt. Fahrettin Koca ya bayyana cewa duk da karin yawan wadanda akeyiwa gwajin Covid-19 a ‘yan kwanakin nan ana ci gaba da samun raguwar masu kamuwa da cutar a rana.

A ranar 22 ga watan Mayu marasa lafiya dubu 1,121 aka samu sun warke inda yawan ya zarta wadanda aka samu dauke da cutar a ranar da dama.

A bisa haka a ranar Juma’ar  ayayinda mutum dubu 1,21 suka warke daga cutar, mutum dubu 952 aka samu dauke da ita.

Kawo yanzu dai a fadin kasar Turkiyya an yiwa mutum miliyan 1,767,495 gwajin kwayar cutar ta Covid-19, daga cikinsu an samu dubu 154,500 dauke da cutar, daga cikin wadanda ke dauke da cutar dubu 116,111 sun warke inda kuma dubu 4,276 suka rigamu gidan gaskiya.Labarai masu alaka