Turkiyya ta aike da kayan taimako zuwa Tunisiya

Turkiyya na ci gaba da aika kayan taimako zuwa kasashen duniya daban-daban domin yaki da annobar Corona (Covid-19).

1413287
Turkiyya ta aike da kayan taimako zuwa Tunisiya

Turkiyya na ci gaba da aika kayan taimako zuwa kasashen duniya daban-daban domin yaki da annobar Corona (Covid-19).

Mahukuntan Turkiyya sun aika da kayan taimako zuwa Tunisiya.

Sanarwar da Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta fitar ta ce "Bayan umarnin da Shugaban Kasarmu Recep Tayyip Edogan ya bayar ne ma'aikatarmu ta shirya kayan taimakodon yaki da Corona tare da tura su zuwa Tunisiya."

Kasar Falasdin ma ta karbi kayan taimakon yaki da annobar Corona (Covid-19) da Turkiyya ta aika mata.

A wajen taron mika kayan da aka gudanar a garin Ramallah na Yammacin Gabar Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye, Ministan Harkokin Wajen Falasdin Riyad Al-Maliki, Jakadan Turkiyya a Kudus Ahmet Riza Demirer da sauran mahukuntan Falasdin sun samu damar halarta.

Minista Al-Maliki ya bayyana cewar wannan taimako da aka ba kasarsu don ci gaba da yaki da Corona na da matukar muhimmanci, kuma suna mika godiyarsu ga Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Ya ce "Wannan taimako na nuni da irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin Shugaban Falasdin Mahmud Abbas da Shugaba Erdogan na Turkiyya."

A ranar 30 ga Afrilu ne jirgin saman daukar kaya na Turkiyya dauke da kayan taimako ga Falasdin ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Gurion da ke kusa da Tel Aviv Babban Birnin Isra'ila.

A baya ma Turkiyya ta aike da kayan taimako don yaki da annobar Corona Covid-19 a kasashen Somaliya, Falasdin, Amurka, Italiya, Spaniya, Kosovo, Makedoniya, Sabiya, Bosniya, Ingila, Afirka ta Kudu, Indonesiya Uganda, Montenegro da sauransu.Labarai masu alaka