Turkiyya ta aika da kayayyakin taimako ga mabukata a Indonesia

Hukumar Bayar da Agagjin gaggawa ta kasar Turkiyya watau Türk Kızılay ta aika da kayayyakin taimako ga mabukata zuwa kasar Indonesiya

1412732
Turkiyya ta aika da kayayyakin taimako ga mabukata a Indonesia

Hukumar Bayar da Agagjin gaggawa ta kasar Turkiyya watau Türk Kızılay ta aika da kayayyakin taimako ga mabukata zuwa kasar Indonesiya.

Hukumar Türk Kızılay ta aika da ton dubu 2 da dari 300 zuwa tsibirin Sulawesi da Sumatra domin rabawa mabukata a watan Ramadana.

Bugu da kari ta shirya wa ma'azumta 300 bude baki a tsibirin  Sumatra.

Hukumar Türk Kızılay, ta ci gaba da kai taimako a tsibirin  Sulawesi tuin bayan afkuwar girgizar kasa da ta kada zukatan al'umman yankin.

A sabili da haka ne hukumar Türk Kızılay, ke gudanar da ayyukan jin kai har guda 12 a tsibirin.

A tsibirin Sulawesi a ranar 28 ga watan Satumba a yankin Palu girgizar kasa mai girman matki 7.5 ta yi sanadiyar rayuka dubu 4 da dari 340.Labarai masu alaka