Shugaba Erdogan ya sanar da sabbin dokokin yaki da Corona a Turkiyya

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da sabbin matakan yaki da cutar Corona (Covid-19) a kasar.

1390910
Shugaba Erdogan ya sanar da sabbin dokokin yaki da Corona a Turkiyya

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da sabbin matakan yaki da cutar Corona (Covid-19) a kasar.

Shugaba Erdogan ya ce daga karfe sha biyun daren sabbin dokokin da Kwamitin Malaman Kimiyya suka bayar da shawara a saka za su fara aiki bayan nazari a kan su da gwamnati ta yi.
Daga cikin dokokin, daga karfe sha biyun dare an hana 'yan kasa da shekaru 20 fita waje a fadin kasar Turkiyya, sannan an hana shiga da fita da ababan hawa a manyan jihohi 31. Duk wadanda ya kama dole su fita waje to sai sun saka abun rufe baki.
Shugaba Erdogan ya kuma ce duk wadanda suka ki aiki da dokar to za su fuskanci hukuncin da ya dace da su.
Ya ce "Manufarmu ba ita ce mu takurawa 'yan kasa ba, ita ce mu kare lafiyarmu da ta wadanda muke mu'amala da su."
Ya ci gaba da cewar "Yadda muka yi aiki da dokokin haka za a samu nasarar yaki da yaduwar cutar cikin gaggawa.
Erdogan ya ce dukkan 'yan kasa ne ke da alhakin tabbatar da lokacinda rayuwa za ta dawo daidai a cikin kasar.


Labarai masu alaka