Turkiyya ta kai karar 'yan kasar Saudiyya 20 bisa kisan gilla ga Kashoggi

Game da kisan gilla ga dan jarida dan kasar Saudiyya Jamal Kashoggi, Turkiyya ta shigar da kara kan mutane 20 'yan kasar Saudiyya.

1384745
Turkiyya ta kai karar 'yan kasar Saudiyya 20 bisa kisan gilla ga Kashoggi

Game da kisan gilla ga dan jarida dan kasar Saudiyya Jamal Kashoggi, Turkiyya ta shigar da kara kan mutane 20 'yan kasar Saudiyya.

Ofishin Mai Gabatar da Kara na Istanbul ne ya fitar da rahoton sakamakon binciken da ya gudanar dangane da kisan dan jarida Jamal kashoggi inda aka lissafo wasu mutane 18.

A takardun bayanan an bukaci da a yankewa mutanen 18 daurin rai da rai kowanne sannan a hada musu da aiki mai wahala.

Haka zalika an bukaci da a daure wasu mutanen 2 da suka ingiza aikata kisan gilla.

A ranar 2 ga watan oktoban 2018 ne aka kashe dan jarida Kashoggi a loakcinda ya je Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Istanbul don karbar takardun aure.

A baya mun bayyana muku cewar dangane da kisan dan jarida Jamal Kashoggi hukumomin Turkiyya sun saka sunayen mutane 20 a cikin bakin littafi.

Ma'aikatar Shari'a ta Turkiyya ta fitar da wata sanarwa ta shafin sada zumunta cewa, an saka sunayen mutane 18 a bakin littafin a watan Nuwamban 2018 sai wasu 2 a watan Disamba.

Sanarwar ta ce, an sanar da Ofishin Sakataren 'Yan sandan kasa da kasa game da lamarin.

A  yanzu haka an fara neman mutanen 20 a kowacce kasa ta duniya.Labarai masu alaka