Cavusoglu: Turkawa 32 sun mutu a kasashen waje sakamakon kamuwa da cutar Corona

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya bayyana cewar Turkawa 32 sun mutu a kasashen waje daban-daban sakamakon kamuwa a cutar Corona (Covid-19).

1384767

Cavusoglu ya bayar da bayanai a Ankara game da Turkawan da aka dawo da su gida daga kasashen waje inda ya ce an yi safara 11 tare da kawo dalibai dubu 2,721 zuwa Turkiyya daga kasashe 8.

Minista Cavusoglu ya ce Turkawa 32 dake kasashen waje sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19), kuma za a kawo gawarwakinsu zuwa Turkiyya.

Ya ce kasashen duniya 69 ne suka nemi taimakon magani daga Turkiyya inda tuni aka aika zuwa kasashe 17.

Cavusoglu ya sanar da tattaunawa ta wayar tarho da Ministan Harkokin Wajen Spaniya inda kasar ta nemi abubuwan rufe fuska daga wajen Turkiyya.

Ya ce "Kamar kowanne lokaci kasashen duniya na bukatar yin aiki tare."

Ya kara da cewar a matsayinsu na kasa suna kokarin sauke dukkan nauyin dake kansu.Labarai masu alaka