Adadin wadanda cutar Corona ta kashe a Turkiyya ya karu

Ya zuwa yanzu mutane 44 ne suka rasa rayukansusakamakon bullar cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.

1384580
Adadin wadanda cutar Corona ta kashe a Turkiyya ya karu

Ya zuwa yanzu mutane 44 ne suka rasa rayukansusakamakon bullar cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.

Ministan Lafiya na Turkiyya Fahrettin Koca ya ce "Mun sake rasa mutanenmu 7, an samu wsu mutanen 343 dauke da cutar."

Minista Koca ya kara da cewar a wanni 24 da suka gabata an yi wa mutane dubu 3,952 gwaji inda ya zuwa yanzu adadin wadanda Corona (Covid-19) ta kama a Turkiyya ya kai mutane dubu 1,872.

Ministan ya ce "Duk da an rasa rai amma Turkiyya ba ta makara ba. Daukar mataki na iya dakatar da yaduwar cutar."

A daidai wannan lokaci kuma dalibai 'yan kasar Turkiyya dake karatu a kasashen Turai kuma suke son dawo wa gida sun shiga kasar.

Daliban sun dawo daga kasashen Ingila, Ailan, Swizalan da Polan da aka hana zuwan jirage daga kasashen suwa Turkiyya.

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Yavuz Selim Kiran ya shaida cewa kamfanin jirgen sama na Turkish Airlines ne ya dakko daliban daga kasashen 4.

Kiran ya yada hotuna daliban a loakcinda suke sauka daga jirgi.

Ya ce "Barkanku da dawowa gidanku. Yanzu lokaci ne na kebe kai da daukar mataki."

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya fadi cewar akwai daliban Turkiyya dubu 3,358 a kasashen Turai 7 da suke son dawowa gida saboda annobar Corona Covid-19.

Cavusoglu ya ce bayan daliban sun dawo za a killace su na kwanaki 14 kafin su shiga cikin jama'a.Labarai masu alaka