Shugaba Erdoğan ya cika shekaru 66 da haihuwa

Dubun-dubatan al'umma sun taya shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan murnar zagayowar ranar haihuwarsa a shafukar sadar da zumunta

Shugaba Erdoğan ya cika shekaru 66 da haihuwa

Dubun-dubatan al'umma sun taya shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan murnar zagayowar ranar haihuwarsa a shafukar sadar da zumunta.

Shugaba Erdoğan wanda aka haifa a ranar 26 ga watan Febrairun shekarar 1954 a yau ya cika shekaru 66 da haihuwa, dubban magoya bayansa sun yada sakonin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa da hashtag  "İyikiDoğdunRTE" a shafukan sadar da zumunta.

Daga cikin wadanda suka taya shugaba Erdoğan murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta 66 sun hada da jami'an gwamnati, 'yan siyasa, 'yan majalisu, jaruman wasan kwaikwayo da jaruman wasannin motsa jiki.

Bikin zagayowar ranar haihuwar shugaba Erdoğan dai ya kasance kan gaba a kanun labaran da suka fita a safiyar yau a fadin kasar Turkiyya.

Wadanda suka taya shugaba Erdoğan murnar cika shekaru 66 da haihuwa sun rinka yada hotunansa daya dauka tare da mahaifiyarsa Tenzile Erdoğan.

 Labarai masu alaka