Sabon tsarin lumana na sanya ‘yan ta’adda mika wuya a Turkiyya

An bayyana cewa sanadiyar sabuwar tsarin samar da lumana da aka dauka 'yan ta'addan PKK na ci gaba da mika wuya ga jami'an tsaro a Turkiyya

1364404
Sabon tsarin lumana na sanya ‘yan ta’adda mika wuya a Turkiyya

An bayyana cewa sanadiyar sabuwar tsarin samar da lumana da aka dauka 'yan ta'addan PKK na ci gaba da mika wuya ga jami'an tsaro a Turkiyya.

An dai dauki hanyar jawo hankalin 'yan ta'addar ne ta yarda zasu tuba su yi nadama su kuma mika wuya.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Turkiyya ce ta sanar da cewa a sakamakon matakan da aka dauka na jan hankalin 'yan ta'adda da hukumomin tsaron kasar Turkiyya suka kaddamar wani kusungumin dan ta'adda da ya tsere a shekarar 2006 mai suna Adem Özdemir ya mika wuya ga jami'an tsaro.

A bisa wannan tsarin wadanda suka mika wuya sun kai 41 a cikin shekarar bana.

 

 Labarai masu alaka