Dangantaka tsakanin Turkiyya da Rasha na cikin mawuyacin halin

Tarihi ya nuna cewa hurda tsakanin Turkiyya da Rasha ya kasance mai hawa da sauka. A lokacin yakin cacar baki ma, ba za’a iya bayyana cewa dangantakar kasashen biyu ta kasance mai kyau ba

1364171
Dangantaka tsakanin Turkiyya da Rasha na cikin mawuyacin halin

Tarihi ya nuna cewa hurda tsakanin Turkiyya da Rasha ya kasance mai hawa da sauka. A lokacin yakin cacar baki ma, ba za’a iya bayyana cewa dangantakar kasashen biyu ta kasance mai kyau ba. Haka kuma, duk da rikicin kakkabawa Turkiyya takunkuman mallakar makamai da Amurka ta yi a shekarar 1964; lamarin da ya sanya Turkiyya kusantar Tarayyar Soviet zamantakewar Turkawa-Rashawa bata kasance mai tagomashi ba. Hakika, a lokacin da yakin cacar baki ya kawo karshe Moscow da Ankara sun samu damar gyara da inganta hurda a tsakaninsu, sai dai rikice-rikicen yankunan Balkan, Bahar Aswad da Caucasia sun kange wacanan damar.  A wananan lokacin bayan karewar yakin cacar baki, ko wace daya daga cikinsu ta dauki sabon salon samun gurin zama a sabuwar tsarin duniya, a sabili da haka dangantakar dake tsakaninsu ta kasa taka kara ta karya balantana ma ta cimma matsayin da suke bukata.

 

A wannan makon a cikin wannan maudu’in mun kasance tare da Daraktan harkokin tsaro Dkt. Murat Yeşiltaş daga Gidauniyar dake nazari akan Harkokin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar dan Adam watau SETA…

 

Duk da sabanin da aka samu an bayyana cewa a shekarar 2000 Turkiyya da Rasha sun yi yunkurin samar da zamantakewa mai kwari a tsakaninsu. A cikin wadannan shekarun duk da dai Moscow na kallon Ankara a matsayar abokiyar hamayyarta bai hana ta kulla yarjejeniyoyi masu gwabi ba kamar su yarjejeniyar kasuwanci a fannukan makamashi. Kasancewar Turkiyya tana makwabtaka da Rasha ya sanya Ankara kulla zamantakewa mai kwari musanman a fannukan iskar gas. A cikin wadanan shekarun, Turkiyya da Rasha sun kusanci juna domin sun ayyanar da hadaka da ayyuka tsakaninsu da dama.

 

Sai dai, a farko-farkon barkewar rikici a Siriya kasashen biyu sun kasance masu kalubalantar juna, daga bisani kuma suka yanke hukuncin aiki akan lamarin tare. Da farko dai kakkabo jirgin yakin Rasha da ya keta hakkin sararin samaniyar Turkiyya a shekarar 2015 ya sanya dangantaka tsakanin kasashen biyu yin tsami gwaran gaske. A sakamakon matakan diflomasiyya da kasashen biyu suka kaddamar a shekarar 2016 sun haifar da sulhu tsakaninsu. Daga waccan ranar kawo yanzu, Turkiyya da Rasha sun kasance  masu daukar dabarun daidaituwa a tsakaninsu. Amma sanadiyar matakan da Rasha ta dauka a cikin ‘yan watannin da suka gabata na taimakawa gwamnatin Siriya da kuma ma ita kanta wajen kai hare-hare ta sama a yankin Idlib daya ragewa ‘yan adawar kasar ya sake fitar da alamar tambaya akan tsanakin hurdar Turkiyya da Rasha.

 

Tabbas dangantakar Turkiyya da Rasha bai kasance akan Siriya kawai ba. A yayinda ake ikirarin cewa Rasha ta yi watsi da yarjejeniyar da ta yi da Turkiyya a Sochi inda ta dauki matakan kauda wadanda ta kira ‘yan tada zaune tsaye a yankin Idlib, ita kuwa Turkiyya ta na neman Rasha ta mutunta yarjejeniyar ta kuma dakatar da gwamnatin Asad daga kai hare-haren a yankin. Idan dai har ba’a dakatar da hare-haren da ake kaiwa a yankin Idlib ba babu yadda Turkiyya zata samu nasarar samar da lumana a yankin.

 

Wannan yanayin ka iya haifar da rigima tsakanin Moscow da Ankara kuma zai iya dakatar da kusantar juna da kasashen biyu ke kokarin yi.

 

Gwamnatin Turkiyya dai na duba muradun dukkaninsu da idon basira; domin kaucewa lamarin da ka iya haifar da rikici a tsakaninsu. Abu na farko dai da ya kusantar da kasashen biyu a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata shi ne maslahar makamin S-400. Duk da kalubalantar lamarin da Amurka ta yi Ankara ta sayi makaman S-400 a gurin Rasha lamarin dake nuni ga  girman  dangantaka a tsakanin kasashen biyu. Bugu da kari, Rasha da Turkiyya na kan tattaunawa akan samar da wata kanfanin tsaro na haddin gwiwa a tsakaninsu. A dayan sashen kuma kasashen biyu, na daukar matakan samawa Turkiyya bukatunta na makamashin nukilya, a wannan tsarin ne Rasha ke kokarin gwada iyawarta a harkokin makamashin nukilya. Wadannan tsarukan biyu zasu inganta harkokin tattalin arzikin Rasha saboda haka a fannukan makamashi dukkanin kasashen biyu dai mabukatan juna ne. Turkiyya dai ce daya daga cikin kasashen dake kan gaba wajen sayen gas din kasar Rasha. Haka kuma bututun iskar gas din Rasha zai ratsa Turkiyya ne zuwa Nahiyar Turai, lamari da ya kasance mai muhinmanci tsakanin kasashen biyu. Hakan na kara nuna cewa kasashen biyu na dogaro ga juna. Turkiyya dai ta kasance aljannar ‘yan yawon bude ido daga kasar Rasha mai sauki. A alkaluman Turkiyya ‘yan kasar Rasha ne suka fi ziyartar kasar a matsayin ‘yan yawon bude ido a shekara da shekaru.

 

Duk da dai rashin jituwa da ake samu akai-akai tsakanin kasashen biyu, lamarin Siriya ya kasance wani abinda ya hadasu guri daya. Ba dai za’a taba samun tsanaki mai inganci a Siriya; ba tare da zaman diflomasiyya da Turkiyya ba koda kuwa Rasha ta ci kashin kanta ta kuma bayyana yin nasarar matakin sojan da take dauka. Ba kuma zai kasance tsari mai kyau ga Rasha ba; ta dauki matakan da zasu sanya farar hula ficewa daga matsugunansu a Idlib su kwarara zuwa Turkiyya domin neman mafaka. Hakan dai mataki ne da zai haifawa Rasha kashe makudan kudade. A ‘yan makonnin da suka gabata Amurka ta fara amfani da wannan damar inda take neman lalata kusantar Rasha da Turkiyya akan maslahar Idlib, musamman ma yadda Amurka ta bayyana cewa zata kasance tare da Turkiyya akan lamurkan Idlib.

 

Idan har Turkiyya da Rasha basu aminta da juna akan lamurkan Idlib ba, ko shakka babu zasu kasance cikin sabuwar rikici kuma za’a samu sabanin kusantar juna da Moscow-Ankara suka kasance suna yi a shekarun da suka gabata. A sabili da haka lamurakn Idlib sun kasance ma’aunin awon danganatakar Turkiyya da Rasha kuma ba lamari ne da ya yi kamada wanda za’a iya warwarewa cikin sauki ba. Idan dai har Rasha na bukatar ci gaba da kyakkyawar hurdarta da Turkiyya ya kamata ta dakatar da matakan kin karin da take dauka a yankin Idlib ta kuma dakatar da hare-haren da gwamnatin kasar ke kaiwa a yankin.

 

Wanann sharhin Dkt. Murat Yesiltas ne Darktan Harkokin Tsaro a Gidauniyar dake nazari akan Harkokin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya.

 Labarai masu alaka