Birnin da ya fi kowanne tsufa a duniya

Ko kun san cewar Istanbul na daya daga cikin birane mafiya tsufa a duniya?

Birnin da ya fi kowanne tsufa a duniya

Istanbul ne kadai birni a duniya da yake da nahiyoyi 2 wato yana cikin Turai da Asiya. Istanbul da ya taba zama cibiyar sakafar Rumawa, Daular usmaniyya, Gabashin Roma da latin ya kasance daya daga cikin birane mafiya tsufa a duniya.

Istanbul da ya fi kowanne birnin yawan mutane a Turkiyya, yana daya daga cikin birane mafiya yawan jama’a 5 na duniya. Istanbul ne birnin da ya fi kowanne habaka a bangaren yawon bde ido a duniya, kuma daya daga cikin masu samun cigaba a fannin kasuwanci.

Akwai muhimman abubuwa da dama game da birnin Istanbul. Daga ciki akwai labarin Halic. A labarin da ake bayarwa a karkashin halic akwai arzikin zinariya kuma a wancan lokacin Japanawa sun so so tsaftace tekun kyauta saboda su samu zinariyar. Bayan gudun hijirar shekarun 1950 zuwa yau fadin “Kasan ıstanbul zinariya ce alla” birnin ya ga yaruka da lahjoji kala-kala. Naa tunanin wancan labarin ne dalilin da ya sanya ake fadin wanan jumla game da birnin.Labarai masu alaka