Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 13.02.2020

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 13.02.2020.

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 13.02.2020

Yeni Safak: "Shugaba Erdogan: Idan aka ci gaba da kai hare-hare, za mu kai hari kan sojojin gwamnatin Siriya a ko'ina ba tare da kallon yarjejeniyar Sochi ba"
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya bayar da sanarwar matakan da ya kamata a dauka a Idlib na Siriya a taron Jam'iyyar AKP. A jawabin nasa ya ce "A nan, ina ayyana cewa idan har sojojinmu a wuraren da ake sanya ido ko kuma a wani wuri suka sami wani karamin rauni, za mu fatattaki sojojin gwamnatin Siriya a ko'ina, ba tare da aiki da yarjejeniyar Sochi ba."

 

Sabah: "Taro mai muhimmanci a Ankara!" Kakakin Shugaban Turkiyya, Ibrahim Kalin ya tattauna da wakilin musamman na Siriya, James Jeffrey. A yayin tattaunawar kan gwamnatin da ke Idlib an bayyana cewa ba a yarda da kai hari a wuraren da Turkiyya ke sanya ido a cikinsu ba. An jaddada alkawarin da Turkiyya ta bayar na kare sojin Turkiyya da fararen hula a yankin Idlib.

 

Star: "Amurka: rage farashin tallace-tallace don cire Turkiyya daga shirin F-35"  
Shugaban Amurka, Donald Trump ya aika da kusan dala tiriliyan 4.8 don kasafin kudin shekarar 2021. Kudin da aka ware wa bangaren tsaro ya ja hankali sosai. Sakamakon cire Turkiyya daga samar da F-35 kudin kayan samar da shi sun karu, amma kudin aikin samar da shi sun ragu.

Haberturk: "Shekarar 2020 ta Patara ce"  
Ma'aikatar Al'adu da Yawon Shakatawa ta zaɓi tsohon birnin Patara da ke Antalya ta gundumar Kash don take-taken shekarar 2020. Tsohon garin wanda aka tabbatar da wanzuwar shi a cikin karni na 8 kafin haihuwar Annabi Isa A.S, yayin da ake binciken tsoffin kayan tarihi shine wurin haifuwa na St. Nicholas wanda ake kira 'Santa Claus'.Labarai masu alaka