Bayanan jami’an gwamnatin Turkiyya akan girgizar kasar data afku a gabashin kasar

Jami'an gwamnatin Turkiyya sun yi yawabai ta sassa daban-daban bayan afkuwar girgizar kasar da ta yi sanadiyar rayuka, raunana fiye da dubu da kuma hasarar dukiyoyi a gabashin kasar

Bayanan jami’an gwamnatin Turkiyya akan girgizar kasar data afku a gabashin kasar

Jami'an gwamnatin Turkiyya sun yi yawabai ta sassa daban-daban bayan afkuwar girgizar kasar da ta yi sanadiyar rayuka, raunana fiye da dubu da kuma hasarar dukiyoyi a gabashin kasar.

Shugaban majalisar kasar Turkiyya Mustafa Sentop ya yada a shafinsa ta Twitter da cewa muna yiwa yan kasarmu Allah ya tsare gaba kuma ma'aikatun ceto zasu ci gaba da aiki tukuru domin saukaka rayuwar wadanda lamarin ya shafa.

Ministan tsaron kasar Hulusi Akar ya bayyana cewa an tura sojojin sama dana kasa a yankin da lamarin ya afku domin bayar da gudunmowar da suka dace.

Ministan makamashi Fatih Donmez ya bayyana cewa an tura masana yankin domin gujewa samon matsalar wutar lantarki da gas.

Ministan Sufuri Cahit Turhan ya yada a shafinsa ta Twitter da cewa Allah ya ji kan wadanda suka rasa rayukansu ya kuma baiwa wadanda suka raunana sauki cikin gaggawa.

Ministan matasa da wasanni Mehmet Muharrem Kasapoglu ya sanar da cewa sun dauki matakan samawa wadanda suka rasa gudajensu mafaka.

Ya kara da cewa an bude cibiyar matasa da gidajen dalibai domin fakewar wadanda lamarin ya shafa a Malatya da Elazig.

Ministan ilimin kasar Ziya Selçuk ya yi adduar Allah ya tsayar nan.

Ministan addinin kasar Ali Erbas ya sanar da cewa wadanda gidajensu suka lalace zasu iya sauka a masallatan dake yankin.

Uwargidan shugaba  Recep Tayyip Erdoğan watau Emine Erdoğan, ta yi adduar samun rahama ga wadanda suka rasa rayukansu da kuma fatar samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka raunana.

Shugaban jam'iyyar MHP Devlet Bahceli ya yada a shafinsa ta twitter da cewa muna goyon bayan matakan da gwamnati ke dauki ina mai matukar imani da cewa za'a yi aiki tukuru domon tono dukkanin wadanda kasa ta taushe.

Haka kuma shugaban jam'iyyar CHP Kemal Kılıçdaroğlu ya yi fatan Alllah ya tsayad nan ya kuma kare gabaLabarai masu alaka