Shugabanin kasashe sun yi wa Turkiyya jaje da ta’aziyya

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yiwa shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan jaje da kuma ta'aziyya akan girgizar kasar da ta afku a gabashin Turkiyya lamarin da ya haifar da hasarar rayuka da dukiyoyi

Shugabanin kasashe sun yi wa Turkiyya jaje da ta’aziyya

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yiwa shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan jaje da kuma ta'aziyya akan girgizar kasar da ta afku a gabashin Turkiyya lamarin da ya haifar da hasarar rayuka da dukiyoyi.

A sakon Putin ya bayyana cewa "Muna masu taya wadanda suka rasa rayukan yan uwansu bakin ciki, muna kuma fatar samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka raunana sanadiyar ibtilair girgizar kasar da ta afku a Turkiyya."

Haka kuma firaministan Kanada Justin Trudeau ya yi jawabi a shafukansa na sadar da zumunta akan girgizar kasa da ta afku a garin Elazig dake kasar Turkiyya.

Ya bayyana cewa "Muna masu adduar ga wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka raunana a girgizar kasar Turkiyya"

Haka kuma ministan harkokin wajen  kasar Yukiren Vadim Pristayko ya a shafinsa ta Twitter da cewa "Muna taya Turkiyya bakin cikin abinda ya afku."

Ministan harkokin wajen Roma  Bogdan Aurescu, ya yada a shafinsa ta Twitter da cewa muna masu bakin ciki akan abinda ya afku muna masu mika taaziyya ga al'umman Turkiyya baki daya.

Ministan harkokin wajen kasar Somalia  Ahmed İsa Avad ya kira ministan harkokin wajen Turkiyya  Mevlüt Çavuşoğlu ta wayar tarho inda ya bayyana bakin ciki game da lamarin tare da yin jaje da mika taaziyyya ga kasar Turkiyya a madadin alumman Somalia baki daya.

 Labarai masu alaka