Shugaba Erdoğan ya ziyarci yankin da girgizar kasa ta afku

Shugaba Recep Tayyip Erdoğan, tare da rakiyar shugaban majalisar Mustafa Şentop, mataimakin shugaban kasa Fuat Oktay da wasu ministoci domin ganarwa ido yanayin yankin garin Sivrice da girgizar kasa mai girman maki 6.8 ta afku ya ziyarci yankin

Shugaba Erdoğan ya ziyarci yankin da girgizar kasa ta afku

 

Shugaban kasar Turkiyya  Recep Tayyip Erdoğan, tare da rakiyar shugaban majalisar kasar  Mustafa Şentop, mataimakin shugaban kasa  Fuat Oktay da wasu ministoci domin ganarwa ido yanayin yankin garin Sivrice da girgizar kasa mai girman maki 6.8 ta afku sun sauka Elazig.

Shugaba Erdogan da ya halarci jana'izar mutum biyu daga cikin wadanda suka rasa rayukansu ya yi jawabi kaman haka.

"Kasar nan taga ire iren girgizar kasa a shekarun baya, kuma alumman kasar nan ta saba jurewa a duk lokacin da ta afku"

Shugaba Erdoğan, ya kara da cewa gwamnatin kasar nan zata yi dukkanin iya kokarinta domin ganin an fitar da dukkanin wadanda kasa ta taushe.

A yayinda yake tsokaci akan hasarar dukiya da gidaje da aka yi ya bayyana cewa hukumar samar da gidaje a kasar zata dukufa domin baiwa wadanda suka rasa matsugunansu muhalli, ba za'a bar kowa a waje ba.

 Labarai masu alaka