Girgizar kasa mai girman maki 6.8 ta afku tare da hallaka rayuka a Turkiyya

Hukumar dake nazari akan girgizar kasa dake Istanbul ta fitar da sanarwar cewa girgizar kasa mai girman maki 6.8 ta afku a gabashin Turkiyya lamarin da ya yi sanadiyar rayuka hudu dangane da bayanan da suka fara fitowa

Girgizar kasa mai girman maki 6.8 ta afku tare da hallaka rayuka a Turkiyya

Hukumar dake nazari akan girgizar kasa dake Istanbul ta fitar da sanarwar cewa girgizar kasa mai girman maki 6.8 ta afku a gabashin Turkiyya lamarin da ya yi sanadiyar rayuka hudu dangane da bayanan da suka fara fitowa.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Turkiyya AFAD ne ta fara bayyana cewa girgizan kasar ta kai girman maki 6.8.

Ministan harkokin cikin gidan Turkiyya Suleyman Soylu ya bayyana cewa sanadiyar girgizar kasar mutun 15 a garin Elazig, 5 kuma a garin Malatya mutane 22 sun rasa rayukansu. Wadanda kuma suka raunana sun kai 1243.

Hukumar AFAD ta bayyana cewa an samu hasara mai yawa inda ta yi kira ga al’umma da su nisanta daga ginukan da suka lalace.

Ministan tsaron kasar Hulusi Akar ya bayyana cewa sojojin kasar shirye suke su kai dauki idan har bukatar hakan ta taso.

Girgizar kasar da ta afku a gabashin kasar Turkiyya ta shafi birane da garuruwan da suka hada da Adana, Osmaniye, Tunceli  Hatay, Mardim, Çorum, Samsun da Tokat da kuma wasu yankunan arewacin Siriya.

An kubutar da mutane fiye da 43 inda ma'aikatan ceto na ci gaba da neman wasu mutum 18.

Hukumar AFAD ta samar da gidajen tafi da gidanka nan take domin fakewar wadanda gidajensu suka rushe sanadiyar girgizar kasar a yankunan.Labarai masu alaka