Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 14.01.2020

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 14.01.2020.

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 14.01.2020

Vatan: "Shugaban Turkiyya Erdogan zai je Jamus"

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan zai ziyarci babban birnin Jamus ranar 19 ga watan Janairu don halartar Taron Berlin. A wajen taron za a tattauna kan cigaban yankin gabashin tekun Bahar Rum da kuma tsagaita wuta a Libiya bayan kokarin Turkiyya. Kasashen da ke halartar taron za su yi musayar ra'ayi kan tsagaita wuta da kuma neman hanyar warware rikicin siyasa a Libiya.

 

Haber Turk: "Kasashen waje na sha'awar Kanal İstanbul"

Ministan Sufuri da Gina Kasa, Cahit Turhan ya bayyana cewa mafi karancin kudin da za a karba duk shekara daga jiragen ruwa da za su ratsa ta mashigar ruwan Istanbul ya kai kusan dala biliyan 1. Ya kara da cewa kamfanonin Holan, Beljiyom da Faransa suna da sha'awar aikin na mashigar ruwan Istanbul, inda ya kuma bayyana dalilan da suka sanya ake buƙatar aikin na mashigar ruwan ta Istanbul. Turhan ya ce hanyar jiragin ruwa ta Bosphorus hanya ce ta ruwa da ake amfani da ita a jigilar jiragen ruwa na kasa da kasa kuma ana fuskantar matsalar zirga-zirgar teku.

 

Sabah: “Hauhawar kudin ruwa a kasuwar hannayen jari ta İstanbul na gudu da lamba daya“

Fata mai kyau wanda ya fara a cikin kasuwannin makon jiya yana ci gaba da karuwa. Duk da yake Kasuwar Hannayen Jari ta Istanbul ya wuce dubu 120 a cikin shekaru 2, ribar ta fadi cikin mafi ƙaranci tun Janairun shekarar 2017 da kashi 10.72 cikin 100. Kimar hadarin Turkiyya na a watanni 20.

 

 

 

 Labarai masu alaka