Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 13.01.2020

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 13.01.2020.

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 13.01.2020

Hurriyet: "Tattaunawa mai mahimmanci a Dolmabahce"

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya karbi bakuncin Firaminista Fayiz es-Sarrac, Shugaban Gwamnatin Hadin Gwiwa (UMH) ta Libiya. A yayin tattaunawar a ofishin shugaban kasa dake Dolmabahce a Istanbul, an tabo batutuwan yarjejeniyar hadin gwiwar soji tsakanin Turkiyya da Libiya.

 

Vatan: "Kakakin Shugaban Turkiyya, Kalın ya fitar da sanarwa kan Libiya"

Kakakin shugaban kasar Turkiyya, Ibrahim Kalin ya bayyana cewa tsagaita wuta a Libiya da birnin Idlib ya faru ne sakamakon ingantacciyar diflomasiyya ta zaman lafiya na Turkiyya. Kalin ya kara da cewa "diflomasiyya tsari ne na aiki. Manufar ita ce tabbatar da zaman lafiya, tsaro, kwanciyar hankali da wadatar kasarmu da yankinmu." 

 

Yeni Safak: "Cavusoglu ya tattauna da takwaransa na Italiya, Maio game da Libiya"

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu da Ministan Harkokin Wajen Italiya, Luigi Di Maio sun tattauna ta wayar tarho. A yayin tattaunawar, sun yi musayar ra'ayi kan abubuwan da suka gabata a Gabashin Tekun Bahar Rum da Libiya.

 

Sabah: "An fara hidimar dakin bacci a tashar jiragenn saman Istanbul"

An fara aikace-aikacen gidan kwanciya a tashar jiragen saman Istanbul wanda kasashen waje suka fara. Hukumar kula da tashar jiragen saman Istanbul, IGA ta fara aikin bayar da izinin gina gidjen kwana mai suna Sleepod ga fasinjoji masu fita daga tashar jirgin saman kasa da kasa don kara kwantar da hankalin fasinjoji. Fasinjoji na iya yin hayar dakin bacci a kan Euro 9 kowacce Sa'a daya.

 

Star: "Turkiyya za ta sami rami ta kasa mafi tsayi"

An kammala yawancin aikin jirgin kasa mai sauri da zai yi tafiya daga Gaziantep zuwa Osmaniye da Adana wanda ya ratsa tazarar mita dubu 9 da dari 8 daga cikin rami na kasa. Shi ne rami na kasa mafi tsawo a Turkiyya, zai rage tafiyar tafiyar awa 5 da mintuna 20 zuwa awa 1 da rabi.Labarai masu alaka