Turkiyya na ci gaba da mayar da 'yan ta'adda zuwa kasansu

An mayar da 'yan ta'adda 11 'yan kasar Faransa zuwa kasarsu.

Turkiyya na ci gaba da mayar da 'yan ta'adda zuwa kasansu

An mayar da 'yan ta'adda 11 'yan kasar Faransa zuwa kasarsu. 

A cikin sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta fitar ta ce ana mayar da 'yan ta'adda na kasashen waje kasashensu.

A wannan karon an mayar da 'yan ƙasar Faransa guda 11.

A gefe guda kuma tun daga 11 ga watan Nuwamba, an mayar da 'yan ta'adda 'yan kasashen waje guda 71 zuwa kasashensu.

Daga 1 ga watan Nuwamba zuwa 9 ga Disamba aka tura 'yan ta'adda 71 kasashensu daga Turkiyya. Daga cikin su akwai Jamusawa 18, Faransawa 11, 'yan Belgium 2, 'yan Holland 2, dan Denmark 1, dan Ostireliya 1, dan Birtaniya 1, dan Amurka 1, da wani dan Ireland.

Ministan Harkokin Cikin Gida Suleyman Soylu, a cikin bayanan da ya yi a ranaku daban-daban ya ce, "ba tare da la’akari da kungiyar ta’addanci za ta tura mambobin kungiyar DAESH ba. Mu ba otal din DAESH ba ne. '' ya kuma bayyana niyyar mayar da 'yan ta'addar kasashen waje zuwa kasashensu.Labarai masu alaka