Harin ta'addanci a Shirnak da ke Turkiyya

A birnin Shirnak da ke Turkiyya jami'an tsaro 2 ne suka mutu, wasu 7 kuma suka jikkata sakamakon fashewar bama-baman da aka samar da hannu da 'yan ta'addar PKK suka dana.

A wata sanarwa da fadar gwamnan Shirnak ta fitar, jami'an Jandarma na gundumar Idil da ke kauyen Sarikoy ta ce an gano bama-bamai da aka samar da hannu da 'yan kungiyar ta'addar PKK suka dana.

Jami'an tsaro 2 ne suka mutu wasu 7 kuma suka jikkata sakamakon fashewar.

Sanarwar ta jaddada cewa ana ci gaba da kai hare-haren yakin ta'addanci a yankin.Labarai masu alaka