Sojojin Turkiyya 2 sun yi Shahada

Sojojin Turkiyya 2 sun yi Shahada a yankunan da ake kai Farmakan Tafkin Zaman Lafiya da Farmakan Pence-3.

Sojojin Turkiyya 2 sun yi Shahada

Sojojin Turkiyya 2 sun yi Shahada a yankunan da ake kai Farmakan Tafkin Zaman Lafiya da Farmakan Pence-3.

Sanarwar da Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta fitar ta bayyana cewar sakamakon harin bam da 'yan ta'addar aware na PKK suka kai a yankin da ake kai Farmakan Tafkin Zaman Lafiya soja 1 ya jikkata, wanda ya kuma rasu a asibitin da aka kai shi duk da kokarin likitoci na ceton ransa.

Sanarwar ta ce a karkashin dokar da ta bayar da damar kare kai an mayar wa da 'yan ta'addar martani inda aka ragargaza wuraren da aka gano suna fake.

A arewacin Iraki da ake ci gaba da kai Farmakan Pence-3 ma 'yan ta'addar awaren na PKK sun jikkata wani soja 1 wanda shi a ya yi Shahada a asibiti.

Sanarwar ta yi Addu'ar samun jin kai ga wadanda suka mutu tare da mika ta'aziyya ga makusantansu.Labarai masu alaka