Turkiyya ta taimakawa yankin da aka yi girgizar kasa a Albenia

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Turkiyya ta aika da rumfunar tafi da gidanka 120, barguna dubu 2 da 750 da wasu kayayyakin tsabta 100 a yankin Albeniya da girgizar kasa ta afku

Turkiyya ta taimakawa yankin da aka yi girgizar kasa a Albenia

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Turkiyya ta aika da rumfunar tafi da gidanka 120, barguna dubu 2 da 750 da wasu kayayyakin tsabta 100 a yankin Albeniya da girgizar kasa ta afku.

An raba wadan nan kayayyakin ga mabukata dake yankin.

Ma'aikatan hukumar bayar da agaji ta kasar Turkiyya da sojojin dake yankin kauyukan Bubq da Tiran a yankin garin Dirach sun ka kafa rumfunar tafi da gidanka domin amfanin wadanda gidajensu suka lalace sanadiyar girgizar kasar.

Shugaban hukumar bayar da agaji ta kasar Turkiyya a Albeniya Anil Kocabal ya bayyana cewar an aika da tireloli biyu zuwa yankin da kayayyakin taimako..

Ya kara da cewa muna tare da alumman Albeniya, kuma za mu ci gaba da bayar da kayayyakin taimako ga kasar.

 Labarai masu alaka