Turkiyya ta mika ta'aziyya ga kasar Ingila

Turkiyya ta yiwa Ingila jaje da ta'aziyya akan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar harin ta'addanci da aka kai a babban birnin kasar Landan

Turkiyya ta mika ta'aziyya ga kasar Ingila

Turkiyya ta yiwa Ingila ta'aziyya akan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar harin ta'addanci da aka kai a babban birnin kasar Landan.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ta yada sakon jajen da ta'aziyya ga kasar ta Ingila.

A sanarwar da ma'aikatar ta yada a rubuce, ta bayyana cewar Turkiyya na matukar bakin cikin samun labarin harin ta'addanci da aka kai a birnin landan lamarin da ya yi sanadiyar rayukan mutane biyu. Hakan na nuni da cewa 'yan ta'adda na ci gaba da nunu bakar aniyarsu na rashin tausayi.

Sanarwar ta kara da cewa, "A cikin wannan mawuyacin halin, muna masu mika sakon ta'aziyya ga hukumar Ingila da muke da kyakyawar hurda da ita. Muna masu yi wa 'yan uwan wadanda suka rasa raukansu ta'aziyya da kuma addu'a samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

A shekaran jiya ne dai aka kai harin ta'addanci da wuka a Gadar Landan lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayuka biyu da raunanan wasu mutane uku.

 Labarai masu alaka