Sojojin Turkiyya 2 sun yi Shahada

Sojojin Turkiyya 2 sun yi Shahada sakamakon harin bam da aka kai musu a cibiyarsu dake gundumar Akcakalen lardin Sanliurfa na iyakar Siriya.

Sojojin Turkiyya 2 sun yi Shahada

Sojojin Turkiyya 2 sun yi Shahada sakamakon harin bam da aka kai musu a cibiyarsu dake gundumar Akcakalen lardin Sanliurfa na iyakar Siriya.

Sanarwar da Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta fitar ta bayyana cewar an mayar da martani nan da nana zuwa ga yankin da aka harbp bam din kuma ana ci gaba da kai farmakai a yankin.

A gefe guda a wani farmaki da Hukumar Leken Asirin Turkiyya (MIT) ta gudanar an kashe wata mace mai suna Beraat Afshin dake da lakabin "Medya Agit" wadda daya daga cikin manyan jagororin 'yan ta'addar PKK/KCK dake arewacin Iraki ne.

A ranar 19 ga Nuwamba aka kashe 'yar ta'addar wadda ake nema ruwa a jallo.

 Labarai masu alaka