Sojojin Turkiyya sun kashe 'yan ta'adda 6 a arewacin Iraki

An kashe 'yan ta'addar a yankunan Zap da Metina dake arewacin Iraki.

Sojojin Turkiyya sun kashe 'yan ta'adda 6 a arewacin Iraki

Dakarun sojin Turkiya sun kai hare-hare ta sama a yankin Zap na arewacin Iraki inda suka kashe 'yan ta'adda 2.

Sanarwar da Ma'aikatar Tsaro ta Turkiyya ta fitar ta shafinta na Twitter ta ce sun kai hari ta sama a yankin Zap na arewacin Iraki.

A harin an kashe 'yan ta'addar aware na PKK 2.

A gefe guda kuma wata sanarwar da Ma'aikatar Tsaron ta fitar ta fadi cewar an kai wasu farmakai a yankin Metina na arewacin Iraki.

A hare-haren an kashe 'yan ta'addar aware na PKK 4.

Ana kuma ci gaba da kai farmakai a yankin.Labarai masu alaka