Altun: An kama dukkan iyalan Al-Bagdadi

Shugaban Sashen Sadarwa na Fadar Shugaban Kasar Turkiyya Farfesa Fahrettin Altun ya bayyana cewar an kama dukkan iyalan Shugaban Kungiyar ta'adda ta Daesh da aka kashe Abubakar Al-Bagdadi.

Sanarwar da Altun ya fitar ta shafinsa na Twitter a cikin harshen Turanci game da kama iyalan na Bagdadi.

Ya ce "Turkiyya ta kama mata da dukkan iyalan shugaban Daesh Bagdadi. masu shakku game da yaki da 'yan ta'addar da Turkiyya ke yi ya kamata su sake duba da tsanaki kan yadda Turkiyya ke yaki da 'yan ta'addar Daesh, PKK, YPG da sauran kungiyoyin ta'adda."

 Labarai masu alaka