Sojojin Turkiyya zasu dakatar da farmakin tafkin zaman lafiya na awanni 120

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu ya bayyana cewar zaia dakatar da farmakın tafkın zaman lafıya har na tsawon kwanaki biyar watau awanni 120

Sojojin Turkiyya zasu dakatar da farmakin tafkin zaman lafiya na awanni 120

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu ya bayyana cewar zaia dakatar da farmakın tafkın zaman lafıya har na tsawon kwanaki biyar watau awanni 120.

Çavuşoğlu ya bayyana cewa wannan dakatawar bawai tsagaita wuta bace, a cikin kwanaki biyar din, barayin kungiyar PKK dake Siriya watau PYD zata janye daga iyakokin Turkiyya-Siriya-Iraki.

Çavuşoğlu ya ayyanar da taron manema labarai jin kadan bayan kammala taron jami'an gwamnat' da tawagar mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence.

A yayinda Cavusoglu ke bayyana cewa an yi yarjejeniya tsakanin tawagar Amurka akan cewa mambobin PYD zasu janye daga iyakokin, za'a tattara makamansu da kuma lalata ginukan da suke amfani dashi ya kara da cewa:

Za'a yi aiki bai daya tare da Amurka a gabashin rafin Firat domin magance kungiyar DEASH a yankunan baki daya.

Ya kuma kara da cewa ba'a yi wata yarjejeniya game da Kobane da Turkiyya ba, inda ya kara da cewa babban manufarmu dai ita ce:

"Mu kakkabe 'yan ta'adda baki dayansu daga yankin gabashin rafin Firat da kuma yankin mai nisan kilomita 32 tare da kuma samar da tsaro da lumana a yankunan da iyakokinmu baki daya" Labarai masu alaka