Ranar 19 ga watan Mayu: Saƙon shugaba Erdoğan ga matasan ƙasar Turkiyya

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yaɗa saƙo akan ranar 19 ga watan Mayu wacce rana ce ta tunawa da Atatürk, matasa da kuma wasanni.

Ranar 19 ga watan Mayu: Saƙon shugaba Erdoğan ga matasan ƙasar Turkiyya

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yaɗa saƙo akan ranar 19 ga watan Mayu wacce rana ce ta tunawa da Atatürk, matasa da kuma wasanni. 

A saƙon mai taken " Ci gaban ƴanci, yancin kai da ƙarfafan Turkiyya" ya jaddada cewa ranar 19 ga watan Mayu rana ce dake nuna tsayin dakar al'umar ƙasar Turkiyya domin ci gaba.

Erdoğan ya ƙara da cewa "ranar 19 ga watan Mayu, ranace da Mustafa Kemal Atatürk ya fita zuwa Samsun domin ƙaddamar da yunƙurin kare ƙasa. Rana ce da aka faɗakar da al'umman ƙasa su kasance tsintsiya maɗaurinki ɗaya, haddin kai da juriya akan ɗaukar matakan korar wadanda suka nemi mamaye ƙasar

Shugaba Erdoğan dake bayyana cewar ranar 19 ga watan Mayu ranace dake ishara ga yanci da yancin kai ya yi kira ga matasa da,

"Kamar yadda jiya ta kasance, a yau ma kune waɗanda zasu tashi tsaye domin kare ƙasar daga mayaudarar yancin da ake bayyani akai. Muna cikin zamanin da ko mai ke canjawa nan take. A cikin wannan yanayin canje-canjen a fannonin kimiyya da fasaha ƙasa na bukatar himmanku da kwarjinin ku, dukkanin mu mana da bukatar ku, domin ɗora ƙasar mu saman wata tafarki muna bukatar shawarar ku, raayoyinku da haɗin kawunanku.

Shugaban ƙasar ya yi kira ga dukkanin al'umar ƙasar da su haɗa kai domin ci da ƙasar gaba bisa tafarkin adalci da yanci.

 

 Labarai masu alaka