Bukukuwan ranar tuna Atatürk a fadin ƙasar Turkiyya

A yau ne ake bukin ranar zagayowar shekara ta 100 da jagora Mustafa Kemal Atatürk ya fita zuwa Samsun domin ƙaddamar da yunƙurin kare ƙasa.

samsun bayrak yuruyus1.jpg
samsun bayrak yuruyus.jpg

A yau ne ake bukin ranar zagayowar shekara ta 100 da jagora Mustafa Kemal Atatürk ya fita zuwa Samsun domin ƙaddamar da yunƙurin kare ƙasa.

Ana bukukuwan wannan rana ta 19 ga watan Mayu a matsayar ranar tuna Atatürk, ranar matasa da wasanni a fadin ƙasar Turkiyya, ofishin jakadodi da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Cyprus barayin Turkiyya.

Ministan matasa da wasanni Mehmet Muharrem Kasapoğlu, ya ziyarci Anıtkabir (Kabarin Atatürk) domin ranar tuna Atatürk, ranar matasa da wasanni na 19 ga watan Mayu.

Ministan ya yi tsayin ban girma a lokacin da ya ziyarci gurin inda kuma ya ajiye fulawan girma.

A yau dai ake gudanar da bukukuwan zagayowar shekara ta 100 da Atatürk ya fita zuwa Samsun a ranar 19 ga watan Mayu 1919.

A wasu guraren da ake gudanarwa da bukukuwan an buɗe tutan Turkiyya mai faɗin mita 1919.

Matasa sun yi tattaki daga garin Atakum zuwa Samsun. A yayinda suke tafiyar sun rera taken daban daban.

 

 Labarai masu alaka