Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 06.12.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 06.12.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 06.12.2018

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, an fara gwajin jirgin yaki na kasa da Turkiyya ta samar na TF-X wanda na cikin jiragen yaki na zamani na 5. Turkiyya dake saurin ta kammala samar da jirgin, na aikin bangarensa na karshe. nan da shekarar 2030 ake sa ran kammala samar da jirgin wanda kuma ya zuwa lokacin ake sa ran samun masu sayan kwaya 400 daga hyannun Turkiyya.

Babban labarin jaridar Yeni Safak na cewa, An fitar da rahoto game da filayen tashi da saukar jiragen sama kusan dubu biyu da suke a kasashe 176 mambobin Majalisar Filayen Tashi da Saukar Jiragen Sama na Turai. An fitar da rahoton na tsakanin 2008-2018. Rahoton ya ce, a cikin shekaru 10 da suka gabata Turkiyya ta kara yawan haduwa da kasashen duniya da kaso 191. Turkiyya ta zama kasar da ta fi zuwa wasu kasashe daga Turai inda yawan wuraren da jiragenta ke zuwa ya karu da kaso 130, zuwa filayen tashi da saukar jiragen sama kuma da kaso 157 sai hade bangarori daban-daban da kaso 534.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, ya zuwa yau ana ci gaba da sauri wajen kera jirgin ruwan yaki na musamman da za a iya yin aiyuka da dama da shi samfurin TCG Anadolu domin amfanin rundunar sojin ruwa ta Turkiyya. Wannan ne aiki mafi girma da a banharen tsaro da Turkiyya take yi ita kadai, kuma hakan na nuna irin karfin da take samu a duniya. An rasge shekara daya a lokacin da aka shirya mika jirgin ruwan ga dakarun Turkiyya inda zai shiga hannunsu a karshen shekarar 2020.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, mutanen da suka shiga Turkiyya daga kasashen waje a watan Oktoban 2018 sun karu da kaso 25.5  idan aka kwatanta da na watan Oktoban 2017. Adadin na wannan karon ya kai mutane miliyan 3.8. 'Yan kasar Jamus na kan gaba a cikin maziyartan inda suka je garin Izmir. Garin Izmir ya karbi 'yan kasashen waje da suka fito daga kasashe irin su Rasha, Faransa, Ingila da Jamus ar su kusan miliyan daya. 'Yan kasar Rasha ne a kan gaba wajen zuwa Turkiyya inda suka kai dubu 604 da 73, kasa ta biyu kuma ita ceJamus mai mutane dubu 589 da 626 inda Ingila ta zo na uku da mutane dubu 264 da 17.Labarai masu alaka